Da duminsa: Kotu ta ce sai Onnoghen ya amsa tuhumar da ake masa

Da duminsa: Kotu ta ce sai Onnoghen ya amsa tuhumar da ake masa

- Kotun da'ar ma'aikata, CCT ta bukaci Alkalin Alkalai na kasa da aka dakatar, Jastice Walter Onnoghen ya zo ya kare kansa a kotu

- Kotun ta bayar da wannan umurnin ne bayan ta yi watsi da bukatar da Onnoghen ya shigar ne neman ayi watsi da karar da aka shigar a kansa

- A hukuncin da ya yanke a yau Juma'a 29 ga watan Maris, Shugaban kotun na CCT ya yi watsi da bukatar da Onnoghen ya shigar a kotun

A yau Juma'a 29 ga watan Maris ne Kotun Da'ar Ma'aikata, CCT tayi fatali da bukatar da Alkalin Alkalai na kasa da aka dakatar, Walter Onnoghen ya shigar a shari'ar da ake masa ya rashin bayyana wasu kadarorinsa.

Shugaban kotun na CCT, Danladi Umar ya ce dole Onnoghen ya gurfana gaban kotun ya kare kansa a ranar 1 ga watan Afrilun 2019.

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisa: Buhari, gwamnoni da shugabannin APC sun lallashi Goje

Da duminsa: Kotu ta ce sai Onnoghen ya amsa tuhumar da ake masa
Da duminsa: Kotu ta ce sai Onnoghen ya amsa tuhumar da ake masa
Asali: Twitter

A baya, Onnoghen ya zargin kotun na CCT da rashin bin ka'ida wurin shigar da karar tuhumarsa da rashin bayyana wasu kadarorinsa.

Da ya ke magana da bakin lauyensa, Cif Adegboyega Awomolo, SAN, Onnoghen ya ce an sabawa doka a wurin bincikarsa gabanin shigar da karar a kotu.

Alkalin Alkalan da aka dakatar ya ce akwai kura-kurai da yawa a cikin karar da aka shigar a kansa inda ya ce ba su da masaniya a kan kadarorinsa da ya bayyana.

Ya ce zargin da ake masa duk tatsuniya ne wanda ba za a amince da su a kotu ba saboda haka ya nemi ayi watsi da karar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa an gurfanar da Onnoghen ne a CCT bayan an shigar da shi kara a watan Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel