Zan bar Najeriya fiye da yanda na same ta - Buhari ga kungiyar CAN

Zan bar Najeriya fiye da yanda na same ta - Buhari ga kungiyar CAN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya tabbaci akan jajircewarsa wajen barin Najeriya fiye da yanda ya same ta a 2015.

Yayinda ya tarbi shugabannin kungiyar ta CAN wacce ta samu jagorancin Rev. Dr. Samson Ayokunle a ranar Juma’a, shugaban kasar ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa zata cigaba da magance muhimman kalubale da kasar ke fuskanta, wanda suka hada da harkar tsaro, tattalin arziki da rashawa.

Kungiyar ta ziyarci fadar shugaban kasa don taya shugaba Buhari murna akan nasarar da ya samu a zabe, sannan shugaban kasar ya fada musu cewa sakamakon zabe da aka kammala kwanan nan, ya nuna yardar da yan Najeriya suke da shi akan shugabancinsa a kasar.

Zan bar Najeriya fiye da yanda na same ta - Buhari ga kungiyar CAN
Zan bar Najeriya fiye da yanda na same ta - Buhari ga kungiyar CAN
Asali: UGC

Yayinda yake bayyana ra’ayinsa akan rawar ganin da kungiyoyin addini suka taka a shekaru hudun da yayi yana mulki, Buhari ya sha alwashin ci gaba da nuna goyon bayan shirye shirye da kungiyar addini ke gabatarwa, mai dauke da manufar kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kai a kasar.

KU KARANTA KUMA: Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Kungiyar Kiristocin Najeeriya (CAN) ta taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna akan nasarar da ya samu wajen sake lashe zaben Shugaban kasa, wanda gudana a watan da ya gabata.

Shugabannin kungiyar, kimanin su 30 karkashin jagorancin Shugaban kungiyar, Dr. Samson Olasupo Ayokunle sun gana da Shugaban kasar ne a fadar Shugaban kasa, a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel