Dokar haramta zanga-zanga a Rivers: Jam'iyyar APC ta mayarwa Gwamna Wike martani

Dokar haramta zanga-zanga a Rivers: Jam'iyyar APC ta mayarwa Gwamna Wike martani

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC reshen Jihar Rivers tayi Allah wadai da dokar hana zanga-zanga da tattaki da gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya saka a jihar.

Jam'iyyar ta fitar da sanarwar ne cikin wata sako da sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mr Chris Finebone ya fitar a garin Fatakwal.

A martanin da tayi a ranar Juma'a, jam'iyyar APC ta ce wannan dokar da gwamnan jihar ya saka "tsabar hauka ne".

DUBA WANNAN: Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita

Dokar haramta zanga-zanga a Rivers: Jam'iyyar APC ta yiwa Gwamna Wike martani
Dokar haramta zanga-zanga a Rivers: Jam'iyyar APC ta yiwa Gwamna Wike martani
Asali: Twitter

Ta kuma ce haramta zanga-zangar ya sabawa doka inda ta tunatar da Gwamna Wike cewa al'ummar Rivers da 'yan Najeriya suna da ikon yin zanga-zangar lumana a karkashin kudin tsarin kasa.

"Gwaman kawai yana abu ne kamar wanda bashi da gaskiya.

"Wani dalilin saka dokar haramta zanga-zangar itace domin baya son duniya ta san irin laifukan da ya tafka a jihar shi yasa ya ke son musgunawa ma'aikatan gwamnati," inji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa akwai yiwuwar masu karbar fansho, ma'aikatan gwamnati, ma'aikatan RDDSA da Greater Port Harcourt City Development Authority da wasu za su fara zanga-zangar saboda rashin kulawa ba su samu daga gwamnatin.

Kamfanin dillancin labarai, NAN ta ruwaito cewa Gwamnatin Jihar Rivers ta saka dokar haramta zanga-zanga a jihar a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

Sanarwar da ta fito daga bakin kwamishinan yada labarai na jihar, Emma Okah ya ce dokar za ta fara aiki nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel