Jam’iyyar PDP tace nasararta a jihar Adamawa cikar burin Atiku ne

Jam’iyyar PDP tace nasararta a jihar Adamawa cikar burin Atiku ne

Jam’iyyar Peoples Democratic Paty (PDP), ta kaddamar da nasarar da dan takararta na kujerar gwamna ya samu a jihar Adamawa a matsayin cikar burin dan takararta na Shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Dan takarar PDP dai a jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ne yayi nasarar lashe zaben da aka gudanar a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

Dama dai tsohon mataimakin Shugaban kasar, Atiku ya dauki alkawarin kwato jihar Adamawa daga hannun jam’iyyar, All Progressibves Congress (APC) mai mulki.

Jam’iyyar PDP tace nasararta a jihar Adamawa cikar burin Atiku ne
Jam’iyyar PDP tace nasararta a jihar Adamawa cikar burin Atiku ne
Asali: Twitter

Dan takarar na PDP, Amadu Umaru Fintiri ya samu nasarar ne da kuri'u 376,552, yayin da gwamna mai ci, Umar Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 336,386.

KU KARANTA KUMA: Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000

PDP ta bayyana farin ciki da wannan nasara da ta samu a shafinta na Twitter, tana mai cewa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar ya cika burinsa na mayar da jihar hannun PDP.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta hadu da wani babban rashi biyo bayan sauya sheka da wani tsohon ministan wasanni da ayyuka na mussamman, Farfesa Taoheed Adeoja yayi, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Tsohon ministan ya sanar da sauya shekarsa daga PDP a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris, a gidansa na Ikolaba da ke Ibadan, jihar Oyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel