Muhimman abubuwa da ya kamata iyaye su sa ni kafin su ba wa yara wayar salula ta zamani

Muhimman abubuwa da ya kamata iyaye su sa ni kafin su ba wa yara wayar salula ta zamani

Mutane da dama su na ganin ba wa yara wayar salula babbar illa ce a wannan zamanin, ya yin da wasu kuma su ke ganin yana da kyau a bawa yaro wayar ta salula, saboda kara wayar musu da kai a rayuwa irin ta wannan zamanin

Shekaru da dama mutane su na ta faman maganganu akan iya shekarun da yaro ya kamata ya kai kafin a ba shi wayar salula ta zamani.

Wasu daga cikin dalilan da suka wo maganganun sun hada da amfani da wayar wurin kallon hotuna da bidiyon batsa, sannan akwai yiwuwar wayar za ta iya salwanta a hannun yaron, ko kuma fadawa tarkon 'yan damfara na yanar gizo.

Muhimman abubuwa da ya kamata iyaye su sa ni kafin su ba wa yara wayar salula ta zamani
Muhimman abubuwa da ya kamata iyaye su sa ni kafin su ba wa yara wayar salula ta zamani
Asali: UGC

Gaskiyar magana dai ita ce, wayar salula ta na da matukar muhimmanci ga rayuwar al'umma musamman wurin sada zumuntaa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga wani taron gaggawa da 'yan kungiyar CAN

Amma zancen dai-dai shekarun da ya kamata a ba wa yaro wayar salula, wannan ya danganta da yanayin yanda iyayen su ka dauki dan na su, saboda shekaru ba su ne abu mafi muhimmanci ba, hankali da tunani, da kuma irin yardar da iyaye su ka yi wa yaro ita ce abu mafi muhimmanci. Kuma su ne abubuwan da ya kamata iyayen sun fahimta kafin su ba shi waya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel