Babbar magana: Buhari ya ki rattaba hannu kan wasu dokoki guda 5

Babbar magana: Buhari ya ki rattaba hannu kan wasu dokoki guda 5

- Shugaba Buhari ya ki rattaba hannu kan wasu dokoki guda biyar da majalisar tarayya ta aike masa domin tabbatar da su a cikin dokokin kasar

- Da wannan sabon ci gaba, adadin dokokin da shugaban kasa ya ki rattabawa hannu a majalisar tarayya ta 8 sun kai 31

A ranar 20 ga watan Maris, Buhari ya ki rattaba hannu akan wasu dokoki biyar da majalisar tarayyar ta gabatar masa

Kwanaki tara bayan da ya yi watsi da wasu dokoki guda biyar, a ranar Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu kan wasu dokoki guda biyar da majalisar tarayya ta aike masa domin tabbatar da su a cikin dokokin kasar.

A cikin wasu wasiku daban daban da ya aikewa shugaban majalisar tarayya, Dr Bukola Saraki, wacce kuma ake sa ran za a karanta ta a mako mai zuwa idan majalisar ta dawo da zama, Buhari ya lissafa dokoki 5 da ya ki rattabawa hannu da suka hada da dokar cibiyar mulkin basussuka ta kasa (2018).

Sauran dokokin sun hada da dokar dokar bunkasa hukumar kanana da matsakaitunb masana'antu (2018); dokar gidauniyar kammala hada kamfanin tama da karafa na Ajaokuta (2018); dokar gidauniyar samar da gidaje a Nigeria (2018) da kuma dokar bankin rance na gwamnatin tarayya (2018).

KARANTA WANNAN: Saboda tsananta tsaro: Gwamna Wike ya kakaba dokar haramta zanga zanga a Rivers

Babbar magana: Buhari ya ki rattaba hannu kan wasu dokoki guda 5
Babbar magana: Buhari ya ki rattaba hannu kan wasu dokoki guda 5
Asali: Depositphotos

Da wannan sabon ci gaba, adadin dokokin da shugaban kasa ya ki rattabawa hannu a majalisar tarayya ta 8 sun kai 31.

A ranar 20 ga watan Maris, Buhari ya ki rattaba hannu akan wasu dokoki biyar da majalisar tarayyar ta gabatar masa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel