Kungiyar CAN ta taya Buhari murnar lashe zabe, ta shawarce shi akan zabar yan majalisa

Kungiyar CAN ta taya Buhari murnar lashe zabe, ta shawarce shi akan zabar yan majalisa

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna akan nasarar da ya samu wajen sake lashe zaben Shugaban kasa, wanda gudana a watan da ya gabata.

Shugabannin kungiyar, kimanin su 30 karkashin jagorancin Shugaban kungiyar, Dr. Samson Olasupo Ayokunle sun gana da Shugaban kasar ne a fadar Shugaban kasa, a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris.

Da yake Magana bayan ganawar da suka yi cikin sirri, Ayokunle yace, kungiyar bata fuskanci kowani matsin lamba ba akan taya shugaba Buhari murna.

Kungiyar CAN ta taya Buhari murnar lashe zabe, ta shawarce shi akan zabar yan majalisa
Kungiyar CAN ta taya Buhari murnar lashe zabe, ta shawarce shi akan zabar yan majalisa
Asali: UGC

Ya bukaci Shugaban kasar da ya bincika fadin kasar don zabar mutane mafi inganci a majalisar, sun kuma addu’an cewa Allah ya kawo ci gaba a kasar karkashin Buhari.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wani taron gaggawa, da shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), a fadarshi da ke Abuja.

KU KARANTA KUMA: Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000

Taron wanda muka samu rahoton an fara shi da misalin karfe 11 na rana, a dai dai lokacin da shugaban kasa ya shiga wurin taron.

A cikin wadanda suka samu halartar taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren tarayya, Boss Mustapha, da kuma wasu daga cikin ministocin shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel