Yanzu Yanzu: PDP ta hadu da cikas yayinda tsohon ministan wasanni ya bar jam’iyyar, ya koma APC

Yanzu Yanzu: PDP ta hadu da cikas yayinda tsohon ministan wasanni ya bar jam’iyyar, ya koma APC

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta hadu da wani babban rashi biyo bayan sauya sheka da wani tsohon ministan wasanni da ayyuka na mussamman, Farfesa Taoheed Adeoja yayi, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Tsohon ministan ya sanar da sauya shekarsa daga PDP a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris, a gidansa na Ikolaba da ke Ibadan, jihar Oyo.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Adedoja yace zai gabatar da wasikar yin murabus daga PDP zuwa ga Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus.

Tsohon ministan yayi bayanin cewa hadewarsa da APC a wannan lokaci don bayar da gudunmawarsa ne wajen tabbatar da hadin kan Najeriya, duba ga cewar akwai Baraka sosai a tsakanin kungiyoyin siyasa da dama a kasar.

Yanzu Yanzu: PDP ta hadu da cikas yayinda tsohon ministan wasanni ya bar jam’iyyar, ya koma APC
Yanzu Yanzu: PDP ta hadu da cikas yayinda tsohon ministan wasanni ya bar jam’iyyar, ya koma APC
Asali: Twitter

Adedoja ya bayyana Seyi Makinde, zababben gwamnan jihar Oyo, a matsayin dan uwansa wanda suke da alaka mai kyau, inda ya kara da cewa ya taya zababben gwamnan murna sannan yana fatan Allah ya shige masa gaba.

KU KARANTA KUMA: Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000

Rahoton ya nuna cewa sauya shekar Adedoja daga PDP, yasa sun zama yan takarar kujerar Shugaban jam’iyyar hudu kenan suka yi murabus daga jam’iyyar.

Sauran sun hada da: Otunba Gbenga Daniel, tsohon darakta janar na kungiyar kamfen din Atiku Abubakar; Farfesa Tunde Adeniran, tsohon mamba a kwamitin amintattu na PDP da kuma tsohon ministan ilimi, da Sanata Rashidi Ladoja na jihar Oyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel