Saboda tsananta tsaro: Gwamna Wike ya kakaba dokar haramta zanga zanga a Rivers

Saboda tsananta tsaro: Gwamna Wike ya kakaba dokar haramta zanga zanga a Rivers

- Gwamnatin jihar Rivers ta bayar da wani sabon umurni na haramtawa al'umma yin zanga zanga a fadin jihar

- Haka zalika ta bukaci dukkanin jami'an tsaro da su tabbata dokar ta yi aiki kan kowa domin tabbatar da tsaron jama'a da kuma kawo kwanciyar hankali

- Rahotanni sun bayyana cewa an samu barkewar rikice rikice har da kisan kai a yayin zabukan jihar da aka gudanar makwannin da suka gabata

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta tattara na nuni da cewa gwamnatin jihar Rivers ta bayar da wani sabon umurni na haramtawa al'umma yin zanga zanga a fadin jihar

Cikin wata sanarwa daga kwamishinan watsa labarai na jihar, Emma Okah, gwamnatin jihar ta ce dokar haramta zanga zangar za ta fara aiki nan take.

Haka zalika sanarwar ta bukaci dukkanin jami'an tsaro da su tabbata dokar ta yi aiki kan kowa domin tabbatar da tsaron jama'a da kuma kawo kwanciyar hankali.

KARANTA WANNAN: Gaskiyar magana: Mun gaji da yawon kiwo - Makiyaya sun sanar da ma'aikatar Noma

Saboda tsananta tsaro: Gwamna Wike ya kakaba dokar haramta zanga zanga a Rivers
Saboda tsananta tsaro: Gwamna Wike ya kakaba dokar haramta zanga zanga a Rivers
Asali: Depositphotos

A ranar Juma'a Mr Okah ya shaidawa jaridar Premium Times cewa zanga zanga na kara yawaita a jihar, kuma da yawansu sun shafi zaben da aka kammala.

"Zanga zangar na kara yawaita, sun mamaye tituna, kungiyoyi da dama na zanga zangar amincewa wasu kuma ta kin amincewa. Idan kuma suka yi haka, suna kawo tsaiko akan tattalin arziki," a cewar Mr Okah.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu barkewar rikice rikice har da kisan kai a yayin zabukan jihar da aka gudanar makwannin da suka gabata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel