Bayan zabe: Kotun koli ta bayyana dan takarar SDP na gaskiya

Bayan zabe: Kotun koli ta bayyana dan takarar SDP na gaskiya

Kotun koli ta yanke hukuncin cewa tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Donald Duke shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben 2019.

Donald Duke ya samu kuri'u 812 inda ya doke abokin karawarsa Farfesa Jerry Gana da ya samu kuri'u 611 a zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Oktoban 2018.

Sai dai Jerry Gana ya tafi kotu inda ya nemi a soke takarar Duke kuma babban kotun da ke babban birnin tarayya Abuja ta yanke hukuncin hakan a Disamban 2018.

DUBA WANNAN: Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe

Bayan zabe: Kotun koli ta bayyana dan takara SDP na gaskiya
Bayan zabe: Kotun koli ta bayyana dan takara SDP na gaskiya
Asali: UGC

Kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin da babban kotun Abuja ta yanke a watan Janairun sai kuma a yau Juma'a 29 ga watan Maris kotun koli ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke na mikawa Donald Duke tikitin takarar jam'iyyar.

Alkalai biyar da suka yanke hukuncin sun hada da Jastis Ejembi Eko, Kudirat Kekere, Amiru Sanusi, Paul Galumje da Uwani Aji.

Kotun ta kuma ce a biya Donald Duke zunzurutun kudi Naira Miliyan 3.

A yayin da Duke da Gana suke fafatawa a kotu, Kwamitin Zartarwa na Jam'iyyar SDP ta goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari gabanin zaben na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel