Za mu fallasa wadanda suka dakile zabe – Kungiyar masu sanya ido

Za mu fallasa wadanda suka dakile zabe – Kungiyar masu sanya ido

Wata kungiya na masu sanya ido akan zaben 2019 mai suna 'Women Advocates Research and Documentation Centre (WARDC)', ta sha alwashin bayyana da kuma kunyata wadanda suka dakile zaben da aka gudanar kwanan nan a kasar.

Kungiyar ta WARDC, tare da hadin kwiyan kingiyar HEDA, sun ce ayyukansu ya tozarta mutuncin kasar a gaban kasashen duniya.

Babban Darektan kungiyar WARDC, Dr Abiola-Afolabi, wanda ya bayyana hakan a jiya, Alhamis a wani taro kan siyan kuri’u da rashawa a siyasa, a Abuja, ta bada shawaran sauraran al’umma, saboda yan Najeriya su samu damar komawa ga hanya madaidaiciya.

Za mu fallasa wadanda suka dakile zabe – Kungiyar masu sanya ido
Za mu fallasa wadanda suka dakile zabe – Kungiyar masu sanya ido
Asali: UGC

Tace: “anyi garkuwa da wassu Jami’an zabe, wassu ma an harbe su. Bana tunanin cewa a tarihin zabenmu za a kai matakin da jami’an zabe baza su iya zama su bayyana sakamakon zabe ba, ba tare da shigar yan bangan siyasa da jami’an tsaro cikin lamarin ba.

KU KARANTA KUMA: Majalisar malamai sun bayyana zaben Kano a matsayin fashin damokradiyya

“Idan muna da rahotanni, me yasa farfesa wadanda ke a matsayin baturen zabe basu fito suyi magana ba. Muna bukatan al’umma su bada kunnuwan su don mutane suyi magana akan abunda ya faru, saboda kada a kuma maimaita hakan.

“Bayan bincike, zamu gabatar da shawarwarin mu ga cibiyoyi da ke da hannu ciki; zamu bayyana sunaye, zamu kuma kunyata wadanda ya kamata suji kunya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel