Majalisar malamai sun bayyana zaben Kano a matsayin fashin damokradiyya

Majalisar malamai sun bayyana zaben Kano a matsayin fashin damokradiyya

Majalisar malamai na jihar Kano ta yi watsi da zaben gwamnan jihar da aka sake a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, ta bayyana shi a matsayin fashin damokradiyya.

A wani jawabi dauke da sa hannun Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, Shugaban kungiyar, yace majalisar malamai na Kano sun yi Allah wadai sannan sun yi watsi da fashin damokradiyya da mutanen Kano suka fuskanta a kwanan nan, da sunan zaben gwamna.

Dr. Kofar Mata ya bayyana cewa, “kamar kowani mai son zaman lafiya a Kano, masu kula da zabe da dama na gida da wajen kasar sun yi korafin cewa zaben wanda ya kamata ya zama na gaskiya da amana, da kuma zaman lafiya ya zamo cike da karya doka."

Majalisar malamai sun bayyana zaben Kano a matsayin fashin damokradiyya
Majalisar malamai sun bayyana zaben Kano a matsayin fashin damokradiyya
Asali: UGC

Majalisar malaman a cikin jawabin ta jero tarin karya doka da aka yi kamar haka: “tarin siyan kuri’u daga yan siyar APC, yaduwar rikici wanda jam’iyya mai mulki ta shirya kuma ta dauki nauyi domin razanarwa da kuma tozarta masu zabe da jami’an PDP.”

KU KARANTA KUMA: Kungiyar CAN na shirin taya Buhari murnar lashe zabe

Har ila yau majalisar tayi korafi akan yadda aka wofantar da na’urar tantance katunan zabe, wanda a cewarta hakan kwace yancn masu zabe ne da kuma hadn bakin jami’an INEC da wasu hukumomin tsaro.

Daga karshe sun yi kira ga gwamnatin tarayya da dukkanin hukumomin da abun ya shafa, da su yi kokarin kwato wa mutane yancinsu domin tabbatar da damokradiyyar kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel