Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke

Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke

- Kotu ta sa a nemo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke a duniya

- Sai dai kuma rahotanni sun nuna cewa tun bayan sakinshi da kotu ta yi, har yanzu ba a san inda ya shiga ba a duniya

Wata babbar kotu a Abuja ta janye belin da aka ba wa shugaban kungiyar ma su kokarin kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, sannan ta ba da damar kamo shi.

A ranar Alhamis ne alkalin kotun, mai shari'a Binta Nyako, ta bayyana kotu ta ba wa Kanu isashen lokaci da ya kamata ace ya bayyana a gabanta domin cigaba da gabatar da shari'arshi, wacce aka ba da belinshi ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 2017.

Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke
Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke
Asali: UGC

Kotu na zargin Nnamdi Kanu da laifuka guda uku, kokarin kafa kungiyar Biafra, da kuma bude kafar ya da labarai ta hanyar da ba ta da ce ba, shi da Bright Chimezie, Chidiebere Onwudiwe, da kuma Benjamin Madubugwu.

KU KARANTA: Duniya ina zaki damu: A Jigawa wani saurayi ya cire kan dan uwanshi akan saniya

Idan ba a mance ba an fara kama Kanu a watan Oktoban shekarar 2015, sannan kotu ta bayar da belinshi bayan shekara da watanni shida yana tsare.

A karshe mai shari'ar ta dage sauraron karar ta shi zuwa ranar 18 ga watan Yulin wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel