Kungiyar CAN na shirin taya Buhari murnar lashe zabe

Kungiyar CAN na shirin taya Buhari murnar lashe zabe

Kungiyar kirstocin Najeriya (CAN), ta musanta batun cewa ana matsa mata lamba akan ta taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zaben Shugaban kasa da yayi a watan Fabrairu.

Kungiyar CAN ta ce, tana nan a kan matsayinta na kungiyar addini kuma zata taya duk wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta bayyana a matsayin wanda yayi nasara a zabe.

Idan za ku tuna a baya mun kawo maku rahoton cewa, daya daga cikin shugabannin kungiyar CAN na kasa, ya yi ikirarin cewa wasu manyan mutane a Gwamnati na cigaba da matsa masu lamba, kan su kai ziyarar taya murna ga shugaban kasar.

Kungiyar CAN na shirin taya Buhari murnar lashe zabe
Kungiyar CAN na shirin taya Buhari murnar lashe zabe
Asali: Facebook

Duk da haka, shugaban kungiyar CAN, Rev. Samson Ayokunle, a wani jawabin da ya gabatar jiya, Alhamis, 28 ga watan Maris ta hannun hadimin sa, Bayo Olajide, yayi watsi da rahoton, inda yake cewa babu wani matsi da suke fuskanta daga kowa.

KU KARANTA KUMA: Bayan lashe zaben jihar Bauchi, EFCC zata dakatad da gurfanar da Bala Mohammed kan badakalar Biliyoyi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, an gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa kada ya bari sojojin babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, su kanannaye majalisar dokokin kasar.

Wani sashi na zababbun sanatoci sun bayyana wa majiyarmu ta Leadership cewa kokarin tsayar da Shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmad Lawan da ake yi a matsayin Shugaban majalisar dattawa, wani makirci ne na son sadaukar da majalisar ga Tinubu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel