Gaskiyar magana: Mun gaji da yawon kiwo - Makiyaya sun sanar da ma'aikatar Noma

Gaskiyar magana: Mun gaji da yawon kiwo - Makiyaya sun sanar da ma'aikatar Noma

- Wasu makiyaya sun roki gwamnati da ta samar masu da kayayyakin da za su taimaka wajen samun matsugunni mai makon yawon kiwon dabbobinsu

- Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa gwamnati ta ce tsarin samawa makiyaya matsugunni zai taimaka ainun wajen dakile rikicin makiyaya da manoma

- Haka zalika makiyayan sun roki gwamnatin da ta gina masu makarantun sakandire domin baiwa 'yayansu damar ci gaba da karatu bayan kammala firamare

A kokarinsu na goyon bayan tsarin killace kiwo, wasu makiyaya sun yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su samar da kayayyakin da za su taimaka wajen ganin sun samu matsugunni guda daya mai makon yawon da suke yi domin kiwon dabbobinsu.

Makiyayan, wadanda suka yi wannan rokon a kauyen Bobii da ke karamar hukumar Mariga a jihar Niger a yayin wata ziyara da ministan noma da bunkasa karkara, Chief Audu Ogbhen ya kai masu, sun ce sun gaji da yawo daga wannan gari zuwa wannan gari, sun zabi zama a waje daya domin kiwon dabbobinsu.

Da ya ke jawabi a madadin makiyayan, shugaban al'umar Fulani mazauna kauyen Bobii, Malam Abu Mairiga, ya ce makiyayan za su goyi bayan dukkanin wani tsari da zai taimaka masu wajen zama a waje daya domin yin kasuwancinsu na dabbobi.

KARANTA WANNAN: Zaben Sokoto: APC ta samu kujeru 16 yayin da PDP ta samu 14 a majalisar dokoki

Gaskiyar magana: Mun gaji da yawon kiwo - Makiyaya sun sanar da ma'aikatar Noma
Gaskiyar magana: Mun gaji da yawon kiwo - Makiyaya sun sanar da ma'aikatar Noma
Asali: Depositphotos

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar daukar tsarin killace makiyaya a waje daya a matsayin hanyar kawo karshen wahalhalun rayuwa da makiyaya ke sha, wadanda ke yawo da dabbobinsu daga wannan waje zuwa wani da nufin neman abinci da ruwa da kuma kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.

A cewar gwamnati, tsarin samawa manoma matsugnni mai dauke da ruwa da ukkanin abubuwan da suke bukata da zai taimaka masu da dabbobinsu zai taimaka ainun wajen dakile duk wani rikici da kiwon nasu ke haddasa da kuma bunkasa kasuwancin na su.

Wasu daga cikin al'umma har ma da wasu gwamnatocin jihohi sun yi Allah-wadai da wannan tsari na killace makiyaya, suna masu ikirarin cewa anyi hakan ne kawai domin mallakar filaye, amma dai mafi yawan masu fashin baki sun raja'a akan tsarin ne zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.

Da ya ke tabbatar da amincewarsu ga wani tsari na gwamnatin tarayyar, musamman na killace makiyayan, Mairiga ya roki gwamnatin da ta gina masu makarantar sakandiren makiyaya domin baiwa 'yayansu damar ci gaba da karatu bayan kammala firamare.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel