Shugaba Buhari ya yi wata muhimmiyyar magana akan tattalin arziki

Shugaba Buhari ya yi wata muhimmiyyar magana akan tattalin arziki

A wata ziyara da tawagar shugaban Jamhuriyar Kongo ta kawo wa shugaba Buhari, shugaban ya yi wata muhimmiyar magana akan hanyar da za abi domin farfado da tattalin arzikin kasashen guda biyu

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewar gwamnatinsa za ta ba wa aiyukan farfado da tattalin arzikin kasa muhimmanci, domin dawo da martabar kasar nan a idon duniya.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar shugaban kasar Jamhuriyyar Kongo, a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari ya yi wata muhimmiyyar magana akan tattalin arziki
Shugaba Buhari ya yi wata muhimmiyyar magana akan tattalin arziki
Asali: Facebook

Ministan harkokin waje na jamhuriyar Kongo, Mista Jean Claude Gakosso, ya bayyana sakon shugaban kasar Kongon, shugaba Denis Sassou Nguesso, ga shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Buhari ya ce "Ina sa ne da halin da kasashen mu su ke ciki, mu na da koma baya a fannin tattalin arziki, sannan za mu yi iya bakin kokarinmu wurin ganin mun dawo da martabar kasashen mu a idon duniyaa, ta hanyar habaka tattalin arzukan mu da kuma kulla alaka mai karfi a tsakaninmu.

KU KARANTA: Duniya ina zaki damu: A Jigawa wani saurayi ya cire kan dan uwanshi akan saniya

A lokacin da ya ke bayyana sakon shugaban kasar ta Kongo, ministan harkokin wajen ya bayyana nasarar da shugaba Buhari ya samu a karo na biyun nan a matsayin babbar nasara.

A karshe tawagar shugaban kasarta Kongo sun yiwa shugaba Buhari addu'ar samun nasara a mulkin da zai gabatar a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel