An kama wasu Fastoci 2 bisa zargin kashe mijin yayarsu

An kama wasu Fastoci 2 bisa zargin kashe mijin yayarsu

Rahotanni sun kawo cewa an kama wasu mutane biyu da ke ikirarin cewa su Fastoci, Chukwuka Stephen da Ejim Stephen, a jihar Ogun bisa zargin kashe mijin yayarsu, Peter Chukwuyem.

Rundunan yan sandan jihar Ogun tayi zargin cewa masu laifin, wadanda suka kasance yan asalin jihar Delta, sun bi sahun surukin nasu zuwa gonarshi a ranar 5 ga watan Febrairu, inda suka sare shi har lahira, saboda ya ki bar masu gaban gidansa domin aiwatar da harkokin cocinsu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, wanda ta tabbatar da lamarin, ya bayyana cewa matar marigayin da matashiyar yarsa ce suka kai rahoton lamarin ga ofishin yan sanda.

An kama wasu Fastoci 2 bisa zargin kashe mijin yayarsu
An kama wasu Fastoci 2 bisa zargin kashe mijin yayarsu
Asali: Depositphotos

Oyeyemi ya bayyana cewa Chukwuyem ne ya kawo Chukwuka, dan shekaru 43, da Ejim, dan shekaru 39, daga kauyen jihar Delta zuwa gidansa a Papa Ibafo, jihar Ogun, don zama tare da iyalinsa.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Mun koyi wasu darusa – Tambuwal

Kakakin yan sandan yace masu laifin sun soma amfani da gaban gidansa don gudanar da ayyukan coci amman ba bisa amincewar surukin nasu ba, don haka sai ya kore su, wanda ya kai ga haifar da rashin jituwa a tsakaninsu.

Kwamishinan yan sanda, Ahmed Iliyasu, ya bada umurnin mayar da masu laifin zuwa sashin kisan kai da sashin kwararru don binciken masu laifin tare da hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel