Mutane 4 sun ji rauni sakamakon hatsarin tanka a ya afku a Ekiti

Mutane 4 sun ji rauni sakamakon hatsarin tanka a ya afku a Ekiti

Mutane hudu ne suka samu rauni a jiya, Alhamis, 28 ga watan Maris lokacin da wata motar tanka cike da man fetur tayi hatsari a Ido-Ekiti, karamar hukumar Ido/Osi da ke jihar Ekiti.

Ababen hawa da dama da aka ajiye a kusa da wurin sun kone kurmus sakamakon man da ya malala daga motar.

Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 9:30am, ya haifar da rudani a garin yayinda mazauna yankin suka kwashe kayayyakinsu domin tsere ma wutan da ya kama a wajen.

Wani idon shaida ya fada ma manema labarai cewa motan ya kwace wa direban ne, inda ya bar kan hanya sannan motar ya dunga dungure.

Mutane 4 sun ji rauni sakamakon hatsarin tanka a ya afku a Ekiti
Mutane 4 sun ji rauni sakamakon hatsarin tanka a ya afku a Ekiti
Asali: Depositphotos

Kakakin hukumar da ke kare afkuwar hatsarurruka a kan hanya, reshen jihar Ekiti, Mista Muhammed Olowo, yace an ceto mutane hudu daga wajen da abun ya afku, sannan aka garzaya da su zuwa asibiti.

KU KARANTA KUMA: An gargadi Buhari kan kada ya bari mutanen Tinubu su kanannaye majalisar tarayya

“Matakin gaggawa da muka dauka ya rage karfin wutan. Koda dai mutane sun ji rani, babu dai wanda ya mutu.

“Mun yi aiki tare sa masu kashe gobara sannan mun yi nasarar daidaita lamura ta hanyar ceto wadanda abun ya cika dasu da kuma tabbatar da zirga-zigan ababen hawa a hanyar,” Inji Olowo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel