Hukumar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 37 a hanyar Abuja

Hukumar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 37 a hanyar Abuja

A kokarin da hukumar 'yan sanda ta ke na yaki da ta'addanci, ta samu damar kama wasu 'yan ta'adda guda 37 da ta ke zargin su da satar da mutane, fashi da makami da kuma tu'ammali da miyagun kwayoyi

Hukumar 'yan sanda shiyyar babban birnin tarayya Abuja, ta kama wasu mutane su 37 da ta ke zargin ma su garkuwa da mutane ne, sannan kuma hukumar ta na zargin mutanen da laifin fashi da makami, da kuma amfani da miyagun kwayoyi.

Kwamishinan 'yan sanda na shiyyar, Bala Ciroma, ya bayyana cewa, bayan kama 'yan ta'addar, hukumar kuma ta yi nasarar ceto wasu yara guda biyu, Rejoice Godwin, da kuma Seke Godwin, wadanda suke 'yan shekaru 7 zuwa 9, rahotanni sun nuna cewa barayin sun sace yaran ranar 8 ga watan Maris dinnan, a wani kauye mai suna Yimi a Zuba.

Hukumar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 37 a hanyar Abuja
Hukumar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 37 a hanyar Abuja
Asali: Twitter

Ya kara da cewa hukumar ta samu nasarar ceto yaran a garin Lambata da ke jihar Niger.

Kwamishinan ya bayyana sunayen wasu daga cikin wadanda ta kama a lokacin da ta ke kokarin kubutar da yaran, inda ya ce: "Akwai Nasiru Mohammed mai shekaru 20; Sale Bello mai shekaru 19; da kuma Hassan Audu mai shekaru 20. An kama su dauke da bindigogi guda biyu. Jami'an sun yi kokarin su kama shugaban 'yan ta'addan wanda ya ranta a na kare," in ji Kwamishinan.

KU KARANTA: Duniya ina zaki damu: A Jigawa wani saurayi ya cire kan dan uwanshi akan saniya

Kwamishinan kuma ya bayyana cewa, bayan wata musayar wuta da jami'an suka yi da 'yan ta'addar, sun samu nasarar kama wani daga cikin barayin da su ka yi kokarin kwace wata bakar mota kirar Mercedes Benz 350.

Sannan ya kara da cewa hukumar ta kara samun nasarar kama wani mai suna Murtala Ibrahim, a ranar 17 ga watan Maris dinnan da misalin karfe 9:30 na dare, akan babbar hanyar Goodluck Ebele Jonathan, a cikin wata bakar mota mai kirar Volkswagen Golf 3, dauke da manyan bama-bamai guda 32.

Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu hukumar ta na gabatar da bincike akan masu laifin, ya ce hukumar 'yan sanda kuma ta canja wani sabon sabo na yaki da ta'addanci a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel