Rahoto na musamman: Adadin kudaden da PENCOM ta tara ya kai Naira tiriliyan 8.67

Rahoto na musamman: Adadin kudaden da PENCOM ta tara ya kai Naira tiriliyan 8.67

- Adadin kudaden da hukumar fansho ta kasa PENCOM ta tara ya kai Naira Tiriliyan N8.67 a wannan shekarar

- PENCOM ta ce shirin karo karo na fansho (CPS), ya zama babbar hanya ga gwamnatin tarayya na samun kudaden gudanar da ayyukan ci gaba

- Mrs Aisha Dahir-Umar ta ce tun bayan da aka kirki PENCOM a shekaru 14 da suka gabata, ba a taba neman ko kobo daga asusun hukumar aka rasa ba

Ya zuwa yanzu, adadin kudaden da hukumar fansho ta kasa PENCOM ta tara ya kai Naira Tiriliyan N8.67 a wannan shekarar, kamar yadda PENCOM ta bayyana tana mai bayar da tabbacin cewa kudaden suna nan a killace.

Mai rikon shugabancin hukumar PENCOM, Mrs Aisha Dahir-Umar, ta bayyana hakan a ranar Alhamis a Akure, babban birnin jihar Ondo a yayin taron tuntuba na jihohi na wata hudun farko na shekarar 2019.

Da ta samu wakilcin shugaban sashen ayyukan jihohi na hukumar, Dr. Dan Ndackson, Dahir-Umar ta bayyana cewa tun daga lokacin da aka fara shirin karo karo na fansho (CPS), ya zama babbar hanya ga gwamnatin tarayya na samun kudaden gudanar da ayyukan ci gaba.

KARANTA WANNAN: Shugabancin majalisar dattijai: APC ta sha alwashin ladabtar da Ndume kan bijire mata

Rahoto na musamman: Adadin kudaden fansho da aka tara ya kai Naira tiriliyan 8.67
Rahoto na musamman: Adadin kudaden fansho da aka tara ya kai Naira tiriliyan 8.67
Asali: UGC

Ta ce tun bayan da aka kirki hukumar fanshon a shekaru 14 da suka gabata, ba a taba neman ko kobo daga asusun hukumar aka rasa ba.

Ta ce tun bayan bukin bude tsarin karo karon fansho na jihohi a 2014, jahohi da dama sun samu ci gaba musamman wajen dora kyakkyawan yakininsu akan shirin na CPS.

Da ya ke bude taron, gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya ce shirin fansho na kasar ya taimaka matuka wajen bunkasa tattalin kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel