An gargadi Buhari kan kada ya bari mutanen Tinubu su kanannaye majalisar tarayya

An gargadi Buhari kan kada ya bari mutanen Tinubu su kanannaye majalisar tarayya

- Wasu zababbun sanatoci sun gargadi Buhari kan kada ya bari mutanen Tinubu su kanannaye majalisar tarayya

- Sun yi zargin cewa kokarin tsayar da Shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmad Lawan da ake yi a matsayin Shugaban majalisar dattawa, wani makirci ne na son sadaukar da majalisar ga Tinubu

- Wani dan majalisa daga Arewa yace yunkurin Tinubu na son mamaye majalisar duk don ya kafa kudirinsa ne na son shugabancin kasa a 2023

An gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa kada ya bari sojojin babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, su kanannaye majalisar dokokin kasar.

Wani sashi na zababbun sanatoci sun bayyana wa majiyarmu ta Leadership cewa kokarin tsayar da Shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmad Lawan da ake yi a matsayin Shugaban majalisar dattawa, wani makirci ne na son sadaukar da majalisar ga Tinubu.

Sun kuma bayyana cewa hakan ce ta kasance a yunkurin da ake na tsayar da Shugaban majalisar wakilai, Hon Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai.

An gargadi Buhari kan kada ya bari mutanen Tinubu su kanannaye majalisar tarayya
An gargadi Buhari kan kada ya bari mutanen Tinubu su kanannaye majalisar tarayya
Asali: UGC

Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole a lokacin taron cin abinci da akayi na zababbun sanatoci aa fadar Shugaban kasa a daren ranar Litinin, ya sanar da Lawan a matsayin dan takarar da jam’iyyar ke so a matsayin Shugaban majalisar dattawa.

Jam’iyyar ta kuma tsayar da Gbajabiamila a matsayin wanda take so ya zama kakakin majalisar wakilai.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Mun koyi wasu darusa – Tambuwal

Daya daga cikin zababbun yan majalisan yace tunda Tinubu ya samar da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Oshiom hole a matsayin Shugaban APC, ya kamata a karrama sauran wadanda suka bayar da gudunmawa wajen nasarar jam’iyyar.

Wani dan majalisa daga Arewa yace yunkurin Tinubu na son mamaye majalisar duk don ya kafa kudirinsa ne na son shugabancin kasa a 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel