Tinubu ko Osinbajp APC zata tsayar takaran shugaban kasa a 2023 - Tanko Yakassai

Tinubu ko Osinbajp APC zata tsayar takaran shugaban kasa a 2023 - Tanko Yakassai

Tsohon dan siyasa, Alhaji Tanko Yakassai, ya bayyana cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta gabatar da tsohon shugaban kasa Yemi Osinbajo, ko Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin yan takarar jam'iyyar a zaben 2023.

Yayinda yake magana da The Interview, Tanko Yakassai ya ce yankin kabilar Yarabawa ta taka rawar gani wajen nasarar shugaba Buhari a zaben 2019.

A kan yiwuwar APC ta zabi dan takara daga yanki Inyamurai a 2023, Yakassai yace da kamar wuya.

A cewarsa: "Lissafe-lissafen shine mataimakin shugaban kasa dan yankin kudu maso yamma ne, akwai wata fahimtar cewa idan Buhari ya kammala wa'adinsa, mataimakinsa na iya zama dan takarar shugaban kasar APC."

"Mataimakin shugaban kasan dan kabilar Yoruba ne. Saboda haka ko ba shi aka gabatar ba, da yiwuwan Tinubu zai zama dan takarar jam'iyyar."

"Kuma bisa ga rashin kokarin da jam'iyyar tayi a yankin kudu maso gabas, ban ga yiwuwan baiwa dan yankin takara ba."

Yayinda yake kare kansa kan goyon bayan Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da yayi a zaben shugaban kasa, dattijon ya ce ya goyi bayan Atiku ne bisa ga kwarewarsa a shugabanci da kasuwanci.

KU KARANTA: Kotu ta yankewa Kansila hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari

Da aka tambayesa: "Ka goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da PDP a zaben da aka kammala. Shin ka yarda cewa Buhari ya lashe zabe da gaske?"

Yace: "A'a. ban yarda ba. Na goyi bayan Atiku saboda ban yi imanin cewa Buhari na da karfi, iko da kwarewan kawo karshen matsalan Najeriya ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel