Zaben 2019: Mun koyi wasu darusa – Tambuwal

Zaben 2019: Mun koyi wasu darusa – Tambuwal

- Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto yace zaben 2019 ya koya masa wasu darusa

- Tambuwal ya sha alwashin cewa zai yi amfani da wannan darusa da ya koya daya bayan daya

- Gwamnan yayi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba inganta jihar ta hanyar yin shugabanci nagari

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal yace zaben 2019 ya koya masa wasu darusa sannan yayi alkawarin amfani da abun da ya koya daya bayan daya.

“Mun koyi wasu darusa, mun koyi darasi sosai, mun ga abubuwa da yawa, kuma amfanin koyon darasi shine aiki da shi,” cewarsa a yayinda ya karbi bakuncin mambobin majalisar jihar da manyan hadimai.

Ya kara da cewa: “Idan ka koyi wani abu amma baka yi amfani da shi ba, toh baka amfana ba daga gare shi kuma ina baka tabbacin cewa mun amfana sosai daga darusan a watanni daya zuwa biyu da suka gabata kuma za mu yi amfani da su."

Zaben 2019: Mun koyi wasu darusa – Tambuwal
Zaben 2019: Mun koyi wasu darusa – Tambuwal
Asali: Twitter

Gwamnan yayi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba inganta jihar ta hanyar yin shugabanci nagari.

“Za mu ci gaba da magance kalubale, mun san abubuwan da suka fi mana muhimmancci, kama daga harkar lafiya, noma, ci gaban jama’a, mun san dukkanin wadannan muhimman abubuwan”, inji shi.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Har ila yau da yake magana da manema labarai a Sokoto, Gwamna Tambuwal ya bayyana ci gaban al’umma a matsayin hanyar karfafa kowani irin ci gaba, inda ya bayyana cewa hakan a matsayin zuba jari wanda ke tasiri mai kyau akan mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel