Sayen kuri'u: Kotu ta yankewa Kansila hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari

Sayen kuri'u: Kotu ta yankewa Kansila hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari

Babban kotun jihar Gambe ta yankewa wani kansilan Bolari ta gabas, a karamar hukumar Gombe a jihar Gombe, hukuncin daurin gidan maza na tsawon watanni uku bisa laifin baiwa masu zabe kudi a rumfar zabe.

Kansilan, mai suna, Ishiyaku Garba, ya dira hannun hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ne inda ta gurfanar da shi a kotun kan zargin laifuka uku.

Hukumar ta bayyanawa kotu cewa an damke Ishiyaku ne bisa ga rahoton cewa yana rabawa jama'a kudi a Bolari, rumfar zabe ta 0077 yayinda ake gudanar da zaben shugaban kasa da mambobin majalisar dokokin tarayya.

Lauya EFCC, S.E Okemini ya ce wannan laifi ya sabawa sashe 124 (5) na dokar zaben 2010 kuma zai fiskanci hukunci.

KU KARANTA: Bayan lashe zaben jihar Bauchi, EFCC zata dakatad da gurfanar da Bala Mohammed kan badakalar Biliyoyi

Da kotu ta tambayi kansilan shin gaskiya ne zargin da ake masa, ya yi na'am da dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Lauyan ya gabatar da shaida, Hillary Obetta, wacce ta gabatar da hujjoji kimanin hudu a kansa.

A shari'ar Alkali Sa'ad Muhammad, ya yanke masa hukuncin wata daya a kurkuku da daman biyan N100,000 na laifin farko, hukuncin daurin wata daya a gidan yari ko tarar N50,000 na laifi na biyu, sannan daurin wata daya a kurkuku ko tarar N20,000.

Sannan kuma alkalin ya bada umurnin cewa kudi N295,000 da aka kwace a hannunsa ta zama dukiyar gwamnatin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel