Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Shugabannin tsaro da shugabannin sauran hukumomin tsaro sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock, a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

A bisa jaridar The Guardian, ba a bayyana ajandar ganawar ba wanda aka yi cikin sirri, koda dai Shugaban kasar yayi ganawa da shugabannin hukumomin tsaro akai-akai, wanda a lokacin ne yake samun bayani akan ci gaban da ke yankunan da suke shugabanta.

Legit.ng ta tattaro cewa shugabannin tsaron da suka halarci ganawar sun hada da; Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonishakin, Shugaban sojin ruwa, Ibok-Ete IIbas; Shugaban sojin sama, Air Marshal Sadiq Abubakar da kuma mukkadashin Shugaban sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu.

Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock
Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock
Asali: Depositphotos

Sai dai an wakilci Laftanal Tukur Buratai, Shugaban hafsan soji da Ahmed Abubakar, daraktan kungiyar liken asiri ne a wajen taron.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben gwamnan Adamawa

Hakazalika taron ya samu halartan ministan tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan-Ali; mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno da kuma daraktan janar na hukumar DSS, Yusuf Bichi.

Ku tuna cewa a baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 5 ga watan Maris, yayi ganawar sirri da shugabannin tsaron kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel