Bayan lashe zaben jihar Bauchi, EFCC zata dakatad da gurfanar da Bala Mohammed kan badakalar Biliyoyi

Bayan lashe zaben jihar Bauchi, EFCC zata dakatad da gurfanar da Bala Mohammed kan badakalar Biliyoyi

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa na shirin dakatad da gurfanar da Sanata Bala Mohammad bayan ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

A dokar kasa, duk wanda aka zaba gwamna ko shugaban kasa yana samun kariya daga kowani irin bincike har sai ya sauka daga mulki.

Bala Mohammed, wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi karkashin Peoples Democratic Party PDP), da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris, ya lallasa gwamna mai ci, Mohammaed Abubakar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Premium Times ta bada rahoton cewa tun lokacin da wa'adinsa ya kare matsayin ministan Abuja a 2015 zuwa wannan watan da ya lashe zabe, Kauran Bauchi yana fuskantar tuhumar zargin cin hanci, rashawa, da taka filaye.

Bayan bincike da aka gudanar, an damke Bala Mohammad a 2016 inda akayi zargin yanada hannu cikin badakalar filaye na kimanin Tiriliyan N1.6tn a birnin tarayya, Abuja.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar APC a jihar Ekiti

An zargeshi da karban cin hancin milyan 550 domin baiwa bankin Aso Savings fili, sannan aka zargesa ba karban wasu milyan 314 daga bankin. A daidai lokacin kuma shine shugaban amintattun bankin.

Sannan aka kara zarginsa da almundahanan miliyan 864 inda aka gurfanar da shi gaban alkalin babban kotun tarayya, Abubakar Talba, a rabar 10 ga watan Mayu, 2017 amma ya samu beli daga baya.

Jaridar Premium Times ta samu labarin cewa akwai wasu bincike da ake gudanarwa wanda ya kunshi badakalar biliyoyi da Bala Mohammad yayi a wannan makon.

Amma bisa ga kariyar da mutanen jihar Bauchi da kundin tsarin mulki suka baiwa duk wanda ya zama gwamna, EFCC ba zata iya gurfanar da shi a kotu domin amsa tambayoyi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel