Yanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben gwamnan Adamawa

Yanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben gwamnan Adamawa

An kammala zaben gwamnan jihar Adamawa a daren ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, inda dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ahmadu Fintiri, ya kayar da gwamna mai ci, Mohammed Bindow.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a sakamakon karshe da aka bayyana daga zaben da aka sake, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 10,480 yayinda APC ta samu kuri’u 1391.

Gaba daya dai jam'iyyar PDP ta samu nasarar ne da kuri'u dubu 376,552, yayin da jam'iyyar APC mai mulkin jihar a yanzu ta zo na biyu da kuri'u 336,386.

A halin da ake ciki, Kwamishinan Zaben jihar, Farfesa Andrew Haruna, ya bayyana Amadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya samu nasarar zama gwamnan jihar a zaben.

Legit.ng ta rahoto da farko cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe rumfar zabe ta 007 da 008 a yankin Bako da ke Yola yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kammala zaben gwamna a jihar Adamawa, a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

Jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 150 yayinda, All Progressives Congress (APC) ta samu kuri’u 68 a mazabar 008.

Yanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben gwamnan Adamawa
Yanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben gwamnan Adamawa
Asali: UGC

Hakazalika a mazabar 007, PDP ta samu kuri’u 185 yayinda APC ta samu kuri’u 60.

KU KARANTA KUMA: Sakamako: PDP lashe zabe a kananan hukumomin Adamawa 14 da aka maimaita zabe

Ana kallon zaben ne a matsayin takara tsakanin manyan yan takara biyu na APC da PDP, wato Gwamna Jibrilla Bindow da Ahmadu Fintiri.

Ku tuna cewa kafin a kaddamar da zaben ranar 9 ga watan Maris a matsayin ba kammalalle ba, Fintiri, tsohon mukaddashin gwamnan jihar, na da kuri’u 367,471, yayinda Bindow ke da kuri’u 334,995, inda hakan yasa dan takarar PDP ke kan gaba da tazara 32,476.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel