Za ayi wa jami'an 'yan sanda tankade da rairaya

Za ayi wa jami'an 'yan sanda tankade da rairaya

A Najeriya hukumar 'yan sanda ta kasa ta ci alwashin kawo wasu gyare-gyare ga jami'anta, ta hanyar karawa wasu mukamai, da kuma ragewa wasu mukamansu, hukumar ta ce za ta gabatar da wannan gyare-gyaren ne, domin dawowa da hukumar martabarta a idon al'umma

Hukumar 'yan sanda ta kasa ta ci alwashin yin gyare-gyare ga jami'anta, wurin ragewa jami'anta mukamai, musamman wadanda suka samu karin girma ta bayan fage.

Rahotanni sun nu na cewa hukumar 'yan sanda ta gama yanke shawara akan ragewa wasu daga cikin jami'anta mukamai, wadanda aka ba wa mukami ba tare da bin yanda doka ta tsara ba.

Za a rage girman 'yan sandan da suka samu mukami ta bayan fage
Za a rage girman 'yan sandan da suka samu mukami ta bayan fage
Asali: Depositphotos

Sannan kuma hukumar ta amince da karawa wasu jami'anta girma, musamman ma wadanda lokacin karin girmansu ya yi amma ba a kara musu ba.

KU KARANTA: Bayan ya sha kaye ya bayyana dalilan da ya sa mulki ba shi da dadi - Gwamnan Bauchi

A bayanin da ya yi tsohon shugaban 'yan sandan na kasa ya ce dole ne a gabatar da wannan kudurin na gyare-gyare a hukumar ko dan a dawo da martabar hukumar 'yan sanda a kasar nan.

Sai dai kuma wasu daga cikin jami'an 'yan sandan da ake sa ran za a rage musu mukaman na su sun nufi kotu da, domin ta dakatar da yunkurin da hukumar ta ke yi na rage musu mukaman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel