Da duminsa: Boko Haram na can garin Chibok suna kone gidajen jama'a

Da duminsa: Boko Haram na can garin Chibok suna kone gidajen jama'a

Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suna nan suna kone gidajen al'umma a mazabar Gatamwarwa da ke karamar hukumar Chibok na jihar Borno.

The Cable ta ruwaito cewa 'yan ta'addan sun shigo kauyen ne misalin karfe 5 na yamma inda suka fara harbe-harbe hakan ya sa al'umma suka rika tserewa domin su tsira da rayyukansu.

Yanzu-yanzu: Boko Haram suna kone gidajen al'umma a Chibok
Yanzu-yanzu: Boko Haram suna kone gidajen al'umma a Chibok
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita

"Sun zo a kan babura masu yawa," wani mazaunin kauyen ya shaidawa The Cable.

"Sun fara harbe-harbe sannan suka fara kone gidaje."

Gatamwarwa kauye ne da ke kilomita 19 daga garin Chibok.

Ku biyo domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel