Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar APC a jihar Ekiti

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar APC a jihar Ekiti

- Kuma dai! Kotu ta kara watsi da Fayose da mataimakinsa

- Kotun ta tabbatar da nasarar Kayode Fayemi matsayin zababben gwamnan jihar Ekiti

Kotun dauaka kara dake zaune a Abuja, ta yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Ekiti, Olusola Kolapo Eleka, ya shigar na kalubalantar nasarar abokin hamayyarsa, Kayode Fayemi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kotun mai alkali uku karkashin jagorancin, Steven Adah, ta yanke cewa hukuncin da kotun zabe ta yanke a ranar 28 ga watan Junairu gaskiya ne kuma ta karawa wannan shari'a karfi.

Kotun zaben jihar Ekiti ta yi watsi da karar PDP inda ta bayyana cewa jam'iyyar hamayyar ta gaza kawo hujjoji kan zargin da take tuhumar APC.

Kayode Fayemi ya sami nasarar zaben ne inda ya samu kuri'u 197,459 amma Kolapo Eleka, ya lashi takobin kwato kujerar a kotu.

KU KARANTA: Kwanaki 13 hannun masu garkuwa da mutane: Abin ba dadi amma na godewa Allah - Alaramma Ahmed Suleiman

A bangare guda, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Osun ta mayar da martani a kan kwace nasarar lashe zaben gwamna daga hannun dan takararta Gboyega Oyetola inda aka mika wa Ademola Adeleke na PDP.

Jam'iyyar ta ce nasarar da kotun sauraron karraakin zabe ta bawa Ademola Adeleke na PDP a matsayin gwamna ba nasara ba ce da za ta dore.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel