Kisan Musulmai 50: An gano kungiyar da maharin New Zealand ke yiwa biyayya

Kisan Musulmai 50: An gano kungiyar da maharin New Zealand ke yiwa biyayya

Sebastian Kurz, shugaban kasar Autria ya bayyana cewar mutumin da ya kashe Muslmai 50 a wani da ya kai Masallatan kasar New Zealand, ya taba bayar da taimakon kudi ga kungiyar da ke rajin bawa farar fata fifiko a kasar Austria.

Shugaba Kurz ya kara da cewa akwai alaka mai karfi tsakanin mutumin da ya kai harin da kungiyar rajin bawa farar fata fifiko a kasar ta Austria.

Martin Sellner, shugaban kungiyar rajin fifita farar fata a Austria, ya karbi tallafin kudi har Yuro 1500 daga hannun wani mutum da sunan sa ya yi daidai da na mutumin da ya kai hari Masallatan birnin Christchurch a New Zealand, kamar yadda mai magana da yawun masu shigar da kasar a Austria ya fada.

A wani faifan bidiyo da shugaban kungiyar ya wallafa a manhajar YouTube, ya tabbatar da cewar ya karbi tallafin kudi da sakon wasika (email) mai dauke da suna irin na maharin kasar New Zealand.

Kisan Musulmai 50: An gano kungiyar da maharin New Zealand ke yiwa aiki
An gano kungiyar da maharin New Zealand ke yiwa biyayya
Asali: Twitter

A cewar sa, yanzu haka zai mika kudin da ya karba daga maharin tun shekarar 2018 ga gidauniyar agaji a kasar Austria.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan sandan kasar Ingila su ka taimaka wajen kwace jihohi 4 daga hannun PDP - Osinbajo

Shugaban kungiyar ya bayyana cewar jami'an 'yan sanda sun kai samame gidansa bisa zargin yana da alaka da maharin na kasar New Zealand.

Shugaban kasar Austria ya bayyana cewar suna duba yiwuwar rushe kungiyar da Sellner ke jagoranta, yayin shugaban kasar New Zealand ya bayyana cewa yanzu haka jami'an 'yan sanda na gudanar da bincike a mai zurfi a fadin kasar da sassan duniya a kan batun harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel