Ihu bayan hari: An karo wa 'yan sanda makamai da kayan aiki bayan Boko Haram sun kai musu hari

Ihu bayan hari: An karo wa 'yan sanda makamai da kayan aiki bayan Boko Haram sun kai musu hari

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno, Damian Chukwu ya bayar da umurnin a karo sabbin makamai a caji ofis-ofis da dakunan ajiye makamai na 'yan sanda a duk fadin karamar hukumar Biu.

Chukwu ya bayar da wannan umurnin ne a ranar Alhamis bayan harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a kauyen Miranga da ke karamar hukumar Biu.

'Yan ta'addan da aka ce sun shigo garin da motocci masu dauke da bindiga guda 10 sun kai hari wani sansanin jami'an tsaro da ke Miringa a yammacin ranar Laraba 27 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Takarar kujerar DSP: Sanatoci 56 suna goyon baya na - Kalu

Ihu bayan hari: An karo wa 'yan sanda makamai da kayan aiki bayan Boko Haram sun kai musu hari
Ihu bayan hari: An karo wa 'yan sanda makamai da kayan aiki bayan Boko Haram sun kai musu hari
Asali: Twitter

Kwashinan 'yan sandan ya ce 'yan ta'addan sun dauki lokaci mai tsawo suna musayar wuta da tawagar jami'an tsaron.

Ya kara da cewa a halin yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba duk da cewa 'yan sandan sun fara bincike a kan lamarin.

A halin yanzu, mazauna kauyen Miringa da suka tsere saboda harin sun fara dawowa muhallinsu.

An ruwaito cewar dakarun sojojin sun fatataki 'yan ta'addan bayan sun fafata na lokaci mai tsawo.

Mazauna garin sunyi kiran neman dauki daga jami'an tsaro misalin karfe 6.30 a lokacin da 'yan ta'addan suka shigo kauyen.

A cewarsu, 'yan ta'addan sun kai farmakin ne a lokacin da musulmin garin ke salla a masallaci inda suka bude wuta suna ta harbe-harbe.

Miranga karamin gari ne da ke karamar hukumar Biu kusa da Buratai, garin su babban hafsin hafsoshin sojojin Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel