Tinubu ya soki yunkurin karin haraji da FG ke shirin yi

Tinubu ya soki yunkurin karin haraji da FG ke shirin yi

Jogara a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rashin amincewar shi da yunkurin gwamnatin tarayya yin kari a harajin kayayakin masarufi wato VAT.

Ya ce yin karin harajin zai kara tsadan kayayaki wanda hakan zai jefa dimbin talakawan Najeriya cikin mawuyacin hali.

"Wannan dalilin yasa na ke kira ga Mr Osinbajo da tawagarsa su saka babban alamar tambaya a kan batun karin harajin VAT ...", inji Tinubu.

DUBA WANNAN: Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe

Tinubu ya soki yunkurin karin haraji da FG shirin yi
Tinubu ya soki yunkurin karin haraji da FG shirin yi
Asali: UGC

Jagoran na jam'iyyar APC ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis wurin taron da aka shirya domin murnar cikarsa shekaru 67 a duniya a dakin taro na kasa da kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Jawabin na tsohon gwamnan jihar Legas din yana zuwa ne sa'o'i kadan bayan Ministan Kudi, Zainab Ahmed ta sanar da cewa gwamnati ta kammala tsare-tsare samun karin kudin shiga ta hanyar kara haraji.

A jawabin da tayi wurin taron jin ra'ayin mutane da kwamitin majalisar dattawa da na wakilai na tarayya suka shirya a ranar Laraba, Mrs Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta bullo da sabon hanyar samun karin kudi domin yin ayyukan da aka zartar a cikin kasafin kudin wannan shekarar.

Ta ce an raba tsarin ne zuwa gida uku kuma ta bukaci hadin kai daga majalisar na tarayya.

Tinubu ya bayar da shawarar a fadada karbar harajin a maimakon yin kari a kan wanda ake biya a yanzu.

"Mu kara fadada karbar harajin saboda mu samu karin kudi. Abinda ya da ce muyi kenan a maimakon muyi karin haraji."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel