Yadda 'yan sandan kasar Ingila su ka taimaka wajen kwace jihohi 4 daga hannun PDP - Osinbajo

Yadda 'yan sandan kasar Ingila su ka taimaka wajen kwace jihohi 4 daga hannun PDP - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana yadda wata tawagar masana kimiyyar fahimtar zane hannu 63 da wasu jami'an 'yan sandan kasar Ingila 50 su ka taimaki tsohuwar jam'iyyar ACN ta kwaci jihohi hudu daga hannun jam'iyyar PDP a shekarar 2007.

Jihohi hudu da Osinbajo ya lissafa an karba daga hannun PDP su ne Osun, Ekiti, Ondo da Edo. Kazalika ya bayyana cewar hatta jihar Ondo da jam'iyyar LP ta kafa gwamnati a lokacin, Bola Tinubu ne ya taimaki Olusegun Mimiko, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar.

Osinabjo na wadannan kalamai ne a wurin bikin taya jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, murnar cika shekaru 67 da haihuwa.

Osinbajo ya yi waiwaye a kan yadda Tinubu ya fada ma sa cewar akwai bukatar su kalubalanci PDP a kotu saboda magudin zabe da ta yi amfani da shi wajen kai wa ga nasara a zaben jihohin kudu maso yamma da jam'iyyar ACN ke da karfi.

"A shekarar 2007, Tinubu ya gayyace ni bayan jam'iyyar ta yiwa ACN magudin zabe a jihohin Ekiti, Osun, Ondo da Edo. Ya fada min cewar zamu iya karbo jihohin mu idan muka tafi kotu.

Yadda 'yan sandan kasar Ingila su ka taimaka wajen kwace jihohi 4 daga hannun PDP - Osinbajo
Osinbajo, Tinubu da Buhari
Asali: UGC

"Na fada wa Tinubu cewar abu ne mai matukar wuya mu iya gamsar da kotu cewar PDP ta yi aringizon kuri'u musamman ganin cewar akwai kuri'u fiye miliyan, amma sai ya ce na je na nemo hanyar da zamu yi amfani da ita.

"Kawai sai na tafi kasar Ingila domin gana wa da kwararru a kan karanta zanen hannun mutane. Bayan na fada masu bukata ta sai wakilin su ya bushe da dariya, tare da shaida min cewar basu taba yin aiki a kan kuri'un zabe da suka wuce 4000 ba amma ina bukatar su yi min aiki a kan kuri'u miliyan 1.3.

DUBA WANNAN: Karin kudin haraji: Tinubu ya gargadi gwamnatin tarayya

"Bayan mun rabu a ranar Alhamis sai ya kira ni ranar Litinin ya shaida min cewar za mu sake magana a kan bukatar da na zo da ita. Bayan mun sake tattaunawa ne aka samu hanyar yin aikin cikin sauki.

"Sai da mu ka dauko hayar kwararru 63, 50 daga cikin su jami'an 'yan sandan kasar Ingila ne. Da kyar Tinubu ya shawo kan hukumomin kasar Ingila ta saki jami'an domin su zo su yi mana aiki a Najeriya - sai da su ka shafe tsawon wata 6 su na aiki.

"Ta hanyar amfani da fasahar sanin zanen hannu mu ka gamsar da kotu cewar PDP tayi nasara ne sakamakon dangwale kuri'u, kuma bisa dogaro da wannan hujja ne kotu ta kwato mana jihohin mu," a cewar Osinbajo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel