Sake zaben Adamawa: PDP ta doke APC a yankin Bako dake Yola

Sake zaben Adamawa: PDP ta doke APC a yankin Bako dake Yola

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe zabe a rumfunan zabe na 007 da 008 a yankin Bako da ke Yola, yayinda hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) ta kammala zaben gwamna da aka sake a jihar Adamawa a yau, Alhamis, 28 ga watan Maris.

PDP ta samu kuri’u 150 inda jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kiri’u 68 a rumfan zabe na 008.

Har ila yau, a rumfan zaben 007, jam’iyyar PDP ta doke APC inda ta ja kuri’u 185, yayinda ta doke APC mai kuri’u 60.

Zaben ya kasance gasa tsakannin dan takaran APC, Gwamna Jibrilla Bindow da Ahmadu Fintiri na PDP.

Ku tuna a baya cewa kafin zaben watan Maris 9 da aka bayyana a matsayin ba kammalalle ba, Fintiri ya samu kuri’u 367,471, sannan Bindow ya samu kuri’u 334,995, wanda ya sanya Shi kan gaba da kuri’u 32,476.

Sake zaben Adamawa: PDP ta doke APC a yankin Bako dake Yola
Sake zaben Adamawa: PDP ta doke APC a yankin Bako dake Yola
Asali: Facebook

Idan kuka kuma lura cewa takardun zabe da aka soke sun kama 40,988, wanda hakan ne yasa hukumar INEC ta sake shirya sake zabe a rumfunan zabe 44 a wuraren rijista 28 da lamarin ya shafa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daga karshe Buhari ya rattaba hannu a mafi karancin albashi 30,000

A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyar APC reshen Adamawa tayi barazanan kaurace ma zaben gwamna da za a sake idan hukumar INEC ta dage kan ranar Alhamis, Maris 28.

Sakataren shirye shirye na APC a jihan, Alhaji Ahmed Lawan, ya bayyana matsayin jam’iyyan ne a ranar Laraba, Maris 27, a Yola, babban birnin jihan

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel