Mutane miliyan 25.6 suka nemi aikin NNPC

Mutane miliyan 25.6 suka nemi aikin NNPC

Akalla mutane miliyan 25.6 suka sallamar da takardun karatunsu yayinda kamfanin man feturin Najeriya NNPC ta alanta neman ma'aikata tun shekarar 2012 da ta nema kuma bata dauki kowa ba.

An rufe shafin daura takardun karatun a ranar Talata, 26 ga watan Maris, 2019.

Wata majiya mai karfi ta bayyanawa Daily Sun cewa yawan mutane milyan 25.6 da suka nemi aikin ya razana shugabannin NNPC da kuma gwamnatin tarayya saboda hakan na nuna cewa akwai babban kalubalen rashin aikin yi a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan cibiyar lissafin Najeriya NBS ta nuna cewa yawan rashin aikinyi a Najeriya ya kara tsanani.

KU KARANTA: Yadda zaben gwamna ke gudana a jihar Adamawa

Rahoton NBS ya nuna cewa yawan mutanen da basu aikin komai ku kuma basu wani aikin kirki ya tashi daga milyan 17.6 a karshen shekarar 2017 zuwa 20.9 a shekarar 2018.

A ranar 13 ga wata Maris, 2018 kamfanin NNPC ta alanta daukan sabbin ma'aikata domin maye guraben kananan ma'aikata, manyan ma'aikata, da shugabanni.

Mun kawo muku rahoton cewa yayinda kamfanin man fetur na kasa watau NNPC ya shimfida ma'auni na shekaru a shirye-shiryen sa na daukar ma'aikata, wani Lauya mazaunin garin Abuja, Mista Pelumi Olajengbesi, ya yi barazanar maka sa a kotu.

Cikin wata wasika da ya aike da ita zuwa ga shugaban kamfanin NNPC na kasa, Dakta Maikanti Baru, Olajengbesi ya yi barazanar maka babban kamfanin a gaban kotu sakamakon yadda ya gindaya shekaru a matsayin ma'auni na daukar aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel