Yanzu Yanzu: Daga karshe Buhari ya rattaba hannu a mafi karancin albashi 30,000

Yanzu Yanzu: Daga karshe Buhari ya rattaba hannu a mafi karancin albashi 30,000

- Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya rattaba hannu a mafi karancin albashi na 30,000 wanda kungiyar kwadago ta nema

- Buhari yace za a fara biyan wannan sabon mafi karancin albashi daga watan Mayu, 2019 don raya ranar ma’ aikata na duniya

Daga karshe Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya rattaba hannu a mafi karancin albashi na 30,000 wanda kungiyar kwadago ta nema.

Shugaba Buhari ya rattaba hannu akan dokar ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

Yanzu Yanzu: Daga karshe Buhari ya rattaba hannu a mafi karancin albashi 30,000
Yanzu Yanzu: Daga karshe Buhari ya rattaba hannu a mafi karancin albashi 30,000
Asali: Depositphotos

Yace za a fara biyan wannan sabon mafi karancin albashi daga watan Mayu, 2019 don raya ranar ma’ aikata na duniya.

A makon da ya gabata ne majalisar dokokin kasar ta gabatar da dokar kasafin kudin.

KU KARANTA KUMA: Ministar kudi tace za a kirkiro karin hanyoyin karbar haraji ga ’yan Najeriya

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Ministan harkokin noma da raya karkara a Najeriya, Audu Ogbeh, ya bayyana cewa a cikin jihohin Najeriya 36 da ake da su, jihohi 11 kacal ne su ka dauki harkar noma da gaske a daidai wannan lokaci.

Cif Audu Ogbeh ya fadawa manema labarai cewa jihohi da-dama a kasar nan ba su dauki batun komawa harkar gona yadda ya kamata ba.

Ministan ya kuma koka da matsalar da ake samu wajen amincewa da kasafin kudi a Najeriya. Audu Ogbeh yake nuna cewa bata lokacin da ake yi a majalisar tarayya kafin a sa hannu a kan kundin kasafin kudin kasar yana da illa ga manoma domin kuwa a cewar sa, tun farkon shekara ya kamata a fara shiryawa aikin damina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel