Tinubu ya bayyana sanadin farin cikin sa yayin murnar cika shekaru 67

Tinubu ya bayyana sanadin farin cikin sa yayin murnar cika shekaru 67

Bola Tinubu, Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya ce yana matukar farin ciki a zagayen ranar haihuwarsa na shekaru 67, bayan ganin yanda jam’iyyarsa ta doke jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Tinubu ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris a lokacin taron da aka saba gudanarwa a kowace shekara don murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Yace: “Bayan godiya ga Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ina godiya ga kwamitin uwar jam’ iyyar kan yin aiki tare da shugabancin jam’iyyar mu don tabbatar da nasarar ga jam’iyyar mu.

Tinubu ya bayyana sanadin farin cikin sa yayin murnar cika shekaru 67
Tinubu ya bayyana sanadin farin cikin sa yayin murnar cika shekaru 67
Asali: Facebook

“Har yanzu muna da shugaban kasa a karo na biyu. Mun kuma lashe yawancin kujerun majalissun kasar. Ina jinjina wa APC.

KU KARANTA KUMA: INEC ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga El-rufai tare da zababbun yan majalisa 34

“Da bamu yi farin ciki ba a bikin ranar haihuwa na ba idan da ace mun kasance kamar wancan jam’iyyar. Amman in matukar farin ciki saboda mun doke su, kuma a matsayina na takwaran shugaban kungiyar yakin neman zabe na kasa kuma masu dabarun jam’iyyar, ina yaba wa kaina. Ina matukar godiya, Bola Tinubu.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel