Ministar kudi tace za a kirkiro karin hanyoyin karbar haraji ga ’yan Najeriya

Ministar kudi tace za a kirkiro karin hanyoyin karbar haraji ga ’yan Najeriya

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, inda ta ce za a bijiro da hanyoyin ne domin samar wa gwamnati kudaden shiga.

Zainab ta bayyana cewa hanyoyin da za a bijiro, za a yi su ne domin samar wa gwamnatin tarayya kudaden shiga. Ya yi wannan jawabin ne a gaban kwamitin majalisar dokokin kasar na kasafin kudi.

A cewarta, ta haka ne za a kara samun kudaden shigar tafiyar da ayyukan Kasafin 2019.

Ministar ta ce an karkasa hanyoyin samun kudaden harajin zuwa gida uku, wadanda ta roki Majalisar Tarayya da su daure su bada goyon bayan shigo da sabbin hanyoyin da za a karbi harajin ga ‘yan Najeriya.

Ministar kudi tace za a kirkiro karin hanyoyin karbar haraji ga ’yan Najeriya
Ministar kudi tace za a kirkiro karin hanyoyin karbar haraji ga ’yan Najeriya
Asali: Depositphotos

Ta ce hanya ta farko ita ce jajircewa da kuma tabbatar da an ci gaba da karbar haraji a inda duk ake ci gaba da karba a yanzu.

A wannan mataki ne Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta dauki tsauraran matakin toshe duk wata kofar da harajin da ya kamata a karba ba ya shiga aljihun gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben gwamna ke gudana a jihar Adamawa

Sannan kuma akwai matakin hada kai da guiwa da masu zuba jari domin samar da kudaden da za a yi ayyukan makamashi da su.

“Ina shaida wa Kwamitin Majalisar Tarayya cewa mun tsara hanyoyin bijiro da samun kudaden shiga ga gwamnati, ta hanyar kara hanyoyin karbar kudaden haraji, wadanda nan gaba kadan za mu dawo majalisa domin mu zauna tare da ku mu tattauna su. Haka kuma za mu kara harajin ‘VAT’’.

Harajin ‘VAT’ dai shi ne harajin jiki-magayi, wanda ake tatsar karin kashi 5 bisa 100 daga hannun kwastoma na adadin kudin kayan da ya saya. Shi ne aka ce za a kara zuwa kashi 7.5 bisa 100.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel