Karin kudin haraji: Tinubu ya gargadi gwamnatin tarayya

Karin kudin haraji: Tinubu ya gargadi gwamnatin tarayya

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya shawarci gwamnatin tarayya a kan ta hakura da yin karin kudin haraji a kan kayayyaki (VAT).

Da yake magana a wurin taron taya shi murnar cikar shekaru 67 da haihuwa, Tinubu ya ce yin karin kudin harajin zai saka 'yan Najeriya cikin wahala.

Ya shawarci gwamnati ta kara fadin hanyoyin shigowar kudaden haraji.

"Dole na fada wa Farfesa Osinbajo da mukarraban sa cewar kar ku kara kudin haraji, zai fi kyau ku fadada hanyoyin shigowar kudi daga haraji.

"Karin kudin haraji a kan kayayyakin amfani zai rage sukunin yin sayayya ga a wurin 'yan Najeriya," a cewar Tinubu.

Karin kudin haraji: Tinubu ya gargadi gwamnatin tarayya
Bola Tinubu
Asali: Facebook

Ministan kasafi a tsare-tsare na kasa, Udo Udoma, ne ya fara furta cewar gwamnatin tarayya za ta kara kudin haraji domin ta samu isassun kudaden da za ta biya sabon karin albashi da majalisa tayi doka a kan sa.

A yayin da 'yan uwa da abokan arziki ke taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwar sa, Legit.ng ta sanar da ku cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika na sa sakon taya murnar ga jagoran jam'iyyar APC na kasa.

DUBA WANNAN: Farfesa Zulum: Sabon gwamnan jihar Borno ya bayyana yadda zai tunkari matsalar BH

Shugaban kasar ya bayyana Tinubu a matsayin daya daga cikin ginshikan dake rike da siyasar Najeriya.

Buhari ya aike da sakon taya murnar ne ta bakin kakakin sa, Femi Adesina.

Shugaba Buhari ya jinjina wa Tinubu bisa sadaukar war sa ga jam'iyyar APC da kuma yaki da rashin adalci kamar yadda ya nuna a lokacin da aka soke zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993, wanda a sakamakon hakan har sai da ya yi gudun hijira, ya bar Najeriya na tsawon wsu shekaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel