Kotu ta yanke wa wani mutun hukuncin wata 1 a kurkuku akan satar N1,840

Kotu ta yanke wa wani mutun hukuncin wata 1 a kurkuku akan satar N1,840

Wata kotun Majistare dake Yaba a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris ta yanke wa Adewunmi Adebanjo, wani mara galihu dan shekara 25 hukunci daurin wata guda a gidan yari, bisa laifin fasa gidan wasu ma’aurata inda ya saci naira 1,840.

Alkalin kotun Oluwatoyin Oghere ya yanke wa Adebanjo hukuncin wata daya a gidan yari ba tare da tara ba.

Oghere ya bada umurnin cewa a mayar wa mai karan kudinsa naira 1,840.

Yan sanda sun kama Adebanjo wanda ke rayuwa a karkashin gadan Ikeja, a ranar 28 ga watan Febrairu da laifin fasawa, shiga da sata.

Mai gabatar da kara, Modupe Olaluwoye, ya fada wa kotu cewa mai laifin a ranar 20 ga watan Febrairu, ya shiga gidan wassu ma’aurata misalin karfe 4 na safe a gida mai lamba 272, Ikorodu road, Shomolu, dake Legas.

Kotu ta yanke wa wani mutun hukuncin wata 1 a kurkuku akan satar N1,840
Kotu ta yanke wa wani mutun hukuncin wata 1 a kurkuku akan satar N1,840
Asali: Twitter

Olaluwoye ya bayyana cewa mai laifin ya shiga gidan wanda ya kawo karan, Mista Ibrahim Yahaya, ya kuma saci naira 1,840 daga akwamar matarsa , Khadijah.

KU KARANTA KUMA: INEC ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga El-rufai tare da zababbun yan majalisa 34

Ta bayyana cewa Adebanjo yayi wa mai karan rauni a hannunsa na dama a yayinda yake yunkurin tserewa.

Ya ce, laifin ya karya sashi 287 da 308(1) na dokar laifuffuka na jihar Legas, 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel