Kotu ta janye belin Nnamdi Kanu, ta bayar da umurnin a cafko shi

Kotu ta janye belin Nnamdi Kanu, ta bayar da umurnin a cafko shi

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta janye belin da aka bawa shugaban kuniyar Indigenous People of Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu a baya.

Alkaliyar kotun, Jastice Binta Nyako ta bayar da umurnin a kamo Nnamdi Kanu.

Kotun ta ce ta bayar da wannan umurnin ne domin Mr Kanu ya ki gabatar da kansa a gaban kotun tun bayan da aka bayar da belinsa a watan Afrilun 2017.

DUBA WANNAN: Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita

Kotu ta janye belin Nnamdi Kanu, ta bayar da umurnin a kamo shi
Kotu ta janye belin Nnamdi Kanu, ta bayar da umurnin a kamo shi
Asali: Facebook

Kotun ta yanke hukuncin cewa dole za a cigaba da sauraron shari'ar inda ta bukaci a tsayar da sabon ranar da za a cigaba da shari'ar ko da ya ke Kanu baya nan.

An dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 18 ga watan Yunin 2019.

Shugaban na kungiyar a ware ta kafa kasar Biafra ya saba ka'idar belinsa ne yayin da ya tsere daga Najeriya ya tafi kasan waje ya buya.

Daga bisani an gano ya tafi kasar Isra'ila ne inda ya rika fitowa a gidajen talabijin da kafafen sada zumunta yana sukar shugabanin Najeriya da gwamnatin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel