INEC ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga El-rufai tare da zababbun yan majalisa 34

INEC ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga El-rufai tare da zababbun yan majalisa 34

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da mambobin majalisan jihar 34

- Kwamishinan hukumar INEC na Kaduna, Alhaji Abdullahi Adamu Kaugama ya gabatar da takardun shaida ga yan majalisa

- Haka zalika Farfesa Antonia ta gabatar wa Gwamna El-rufai tare da mataimakiyar sa Hadiza Balarabe Abubakar

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC), a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da mambobin majalisan jihar 34.

An gudanar da taron ne a sakateriyar hukumar, wanda ke a Unguwar Rimi GRA a bainar kwamishinan hukumar INEC na kasa mai kulawa da jihohin Plateau, Niger, Abuja da Kaduna, Farfesa Antonia Okoosi-Simbine da sauran manyan jiga-jigan gwamnati.

Tace zabbukan Najeriya sun soma inganta kuma yana ci gaba da samun yawan masu takara ganin yanda zabbukan suka gudana.

INEC ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga El-rufai tare da zababbun yan majalisa 34
INEC ta gabatar da takardun shaidan cin zabe ga El-rufai tare da zababbun yan majalisa 34
Asali: UGC

Ta kuma yi korafi akan yanayin tashin hankali a wassu jihohi a lokacin zabbuka, ta kuma yabawa al’umman Kaduna akan yanda suka gudanar zabe cikin kwanciyar hankali.

Jami’ar hukumar INEC din har ila yau ta yabawa zababbun yan majalisa daga kananan hukumomi 23 dake a jihar.

KU KARANTA KUMA: INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Gwamna Ishaku da zababbun yan majalisan Taraba 24

Kwamishinan hukumar INEC na Kaduna, Alhaji Abdullahi Adamu Kaugama ya gabatar da takardun shaida ga yan majalisa yayin da Farfesa Antonia ta gabatar wa Gwamna El-rufai tare da mataimakiyar sa Hadiza Balarabe Abubakar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel