Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta yi watsi ada bukatar da ke neman a sake kirga takardun zaben Ogun

Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta yi watsi ada bukatar da ke neman a sake kirga takardun zaben Ogun

Kwamitin mutane uku da ke sauraron karar zaben majalisar dokokin kasa a Abeokuta, jihar Ogun karkasshin jagorancin Justis Elvis Ngene, ta yi watsi da bukatar da ke neman a sake kirga takardun zabe da aka yi amfani dasu a yankin Ijebu Ode/Odogbolu/Ijebu da ke jihar Ogun.

Justis Ngene, yayin da yake yanke hukunci akan batun da masu karan; Taiwo Shote da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka kawo, yace hakan bai yi dai dai da sashi na 151 na dokar zabe ba.

A cewar shi, dokar zaben ta bayyana irin umurnin da kotun ke iya bayarwa, wanda kuma bai wuci binciken kayan zabe da kuma samun ainihin takardun kayayyakin ba.

Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta yi watsi ada bukatar da ke neman a sake kirga takardun zaben Ogun
Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta yi watsi ada bukatar da ke neman a sake kirga takardun zaben Ogun
Asali: UGC

Har ila yau, ya bayyana cewa kotun na tafiya ne shawarar kotun daukaka kara akan lamarin, wanda a cewar shi ba a gwada ta ba a matakin kotun koli.

KU KARANTA KUMA: INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Gwamna Ishaku da zababbun yan majalisan Taraba 24

Lauyan mai kara, Esom Ifeoma ta roki kotun da ta bada umurnin sake kirga takardun zaben da aka yi amfani dasu a zaben, daga cikin sauran rokon da lamarin ke dauke dasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel