Muna fuskantar matsin lamba kan taya Buhari murna - CAN

Muna fuskantar matsin lamba kan taya Buhari murna - CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), tayi zargin cewa wasu manyan mutane masu kusanci da Gwamnatin Tarayya na matsa ma shugabannin kungiyar, akan su kai ziyarar taya murna ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lashe zaben da yayi a watan da ya gabata.

Wani majiyi a majalisan shugabancin kungiyar CAN na kasa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce matsin har ya kai ana yiwa shugabannin kungiyar bita da kulli.

“Idan ka san irin matsi da aka daura ma shugabancin kingiyar CAN cewan mu, a matsayin kungiya, dole mu taya shugaban kasa murna. Duk da haka, coci tana fadin cewa wannan zaben ya kasance da rigingimu kuma mun ga abunda ke faruwa. Kuma har ila yau ana matsa mana lamba.

Muna fuskantar matsin lamba kan taya Buhari murna - CAN
Muna fuskantar matsin lamba kan taya Buhari murna - CAN
Asali: Facebook

“Suna fada mana da cewa idan har bamu taya shi murna ba, wannan yana nufin bamu tare da shi kuma muna mara wa jam’iyya baya. Duk da haka muna fadin cewa su bari kotu ta yanke hukuncci akan wannan lamarin kafin mu taya duk wanda yayi nasara murna. Yanayin da muka tsinci kanmu kenan a matsayin cocin Allah.”

A wani lamari kuma, shugaban kungiyar CAN, Rev. Samson Ayokunle, yayi Allah wadai da garkuwa da akayi da wani fasto katolika, Fr. John Shekwolo, a jihar Kaduna.

KU KRANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ko sama ko kasa ba a ga Buhari ba a wajen taron Tinubu

Yace abun kunya ne ace “yan bindiga suna cigaba da garkuwa da mutane har ma wassu lokutan su kashe al’umma ba tare da laifi ba kuma ba tare da an hukunta su ba.”

Ya jaddada bukatan sake tsara yanayin cibiyoyin tsaron Najeriya sannan shirya shuwagabannin hukumomin tsaro don fidda kasar daga yanayi mai tsanani da take ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel