Babu abin da za ku tashi da shi a Majalisa – APC ta nanatawa PDP

Babu abin da za ku tashi da shi a Majalisa – APC ta nanatawa PDP

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake jadadda cewa Sanata Ahmad Lawan ta ke so ya zama shugaban majalisar dattawa. APC tayi wannan magana ne ta bakin Kakakinta watau Lanre Isa-Onilu.

A jiya Laraba 27 ga Watan Maris, jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa ta riga ta yanke hukunci game da kujerar shugaban majalisar dattawa inda ta ce Sanata Ahmad Lawan ta ke so ta gani a kan wannan kujera a majalisa ta 9.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Mista Lanre Isa-Onilu, yayi wannan jawabi a lokacin da ya gana da manema labarai a sakatariyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja. Onilu yace APC tana nan kan bakar ta.

Jam’iyyar tace ta riga ta gama yanke hukunci game da takarar Ahmad Lawan don haka ya ragewa Sanatocin jam’iyyar su fito su san yadda za su yi domin ganin ya dare kan wannan kujera da zarar an kafa sabuwar majalisa a kasar.

KU KARANTA: A bar maganar: Oshiomhole yana nema Kotu tayi watsi da zargin da ke kan sa

Babu abin da za ku tashi da shi a Majalisa – APC ta nanatawa PDP
Ahmad Lawan kurum mu ka sani a takarar majalisar dattawa inji APC
Asali: Twitter

Haka zalika jam’iyyar mai mulki ta nanata cewa babu abin da zai sa ta raba kujerun shugabancin majalisar tare da jam’iyyar hamayya ta PDP wanda ba ta da rinjaye a majalisar tarayyar. Isa-Onilu yace APC za ta rike duk mukaman.

Mista Isa-Onilu ya kuma kara da cewa PDP ba za ta samu mukaman kwamitin da ake kira masu tsoka a wannan majalisar ba. Kakakin jam’iyyar yace babu yadda za ayi jama’a su zabi APC, sai kuma PDP ta zo ta karbe majalisa a hannun ta.

Jam’iyyar mai rinjaye tace nan gaba kadan za ta fito ta fadi yadda ta kasa sauran mukaman majalisar dattawan da kuma wadanda ta ke so a ba mukamai a majalisar wakilai ta tarayya a wannan karo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel