Yanzu Yanzu: Ko sama ko kasa ba a ga Buhari ba a wajen taron Tinubu

Yanzu Yanzu: Ko sama ko kasa ba a ga Buhari ba a wajen taron Tinubu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron Bola Tinubu ba, babban jigon jam'iyyar APC

- An shirya taron ne domin raya ranar haihuwarsa

- Ba a san dalilin rashin zuwan Shugaban kasar wajen taron ba amma dai mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinabajo ya tsaya wa Buhari wanda ya kamata ya zama Shugaban taron

Ko sama ko kasa ba a ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a wajen taron Bola Tinubu, Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ana gudanar da taron ne duk shekara, domin raya ranar haihuwar tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Taron wannan shekarar, wanda aka sanya wa taken “Next Level: Work For People”, na gudana ne a cibiyar ICC, Abuja.

Yanzu Yanzu: Ko sama ko kasa ba a ga Buhari ba a wajen taron Tinubu
Yanzu Yanzu: Ko sama ko kasa ba a ga Buhari ba a wajen taron Tinubu
Asali: Facebook

Ba a san dalilin rashin zuwan Shugaban kasar wajen taron ba amma dai mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinabajo ya tsaya wa Buhari wanda ya kamata ya zama Shugaban taron.

Buhari ya halarci taron na shekarar bara da wadanda suka gudana a baya a Lagas.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar SIVWOC ta kai karar ‘Yan takarar Bauchi gaban Shugaban kasa Buhari

Akwai wasu rahotanni da ba a tabbatar ba wanda ke nuna cewa Shugaban kasar baya kasar. Jariar TheCable ta ruwaito.

Taron wannan shekarar zai mayar da hankali wajen tattauna ayyuka da tattalin arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel