Bayan ya sha kaye ya bayyana dalilan da ya sa mulki ba shi da dadi - Gwamnan Bauchi

Bayan ya sha kaye ya bayyana dalilan da ya sa mulki ba shi da dadi - Gwamnan Bauchi

Ba sosai aka cika samun masu mulki su na korafi akan mulki ba musamman ma masu mulki na wannan lokaci, to sai dai kuma sai ga gwamnan Bauchi Mohammed A Abubakar ya bayyana wasu abubuwa guda biyar da ba ya jin dadinsu a mulkin da ya yi

A wata hirar bidiyo da gwamnan jihar Bauchi wanda ya sha kaye a yanzu ya yi da manema labarai, ya bayyana wasu dalilai guda biyar da suka sanya mulki ba shi da dadi.

Bayan ya sha kaye ya bayyana dalilan da ya sa mulki ba shi da dadi - Gwamnan Bauchi
Bayan ya sha kaye ya bayyana dalilan da ya sa mulki ba shi da dadi - Gwamnan Bauchi
Asali: Depositphotos

Ga bayanin da ya yi wa 'yan jaridar:

"A cikin harkokin gudanar da mulki, akwai abubuwan da ba su da dadi."

Matsala ta daya: Nisa da iyali da kuma dangi

Aiki ne wanda zai dauke ka daga 'ya'yanka da kuma sauran 'yan uwanka. Saboda akwai wani abu da ya faru da ni, na yi tafiya na yi wajen sati biyu ba na nan, ina da dana wanda watanninsa wajen biyar ne ko shida, ina dawowa da nazo na dauke shi ya zura min ido, sai ya dauke kansa yana nema ya yi kuka, saboda bai gane ko wanene ni ba.

Matsala ta biyu: Yin taro da tsakar dare

Taro na tsakar dare shi ma yana da illa matuka.

Matsala ta uku: Rashin samun lokacin kanka

Rashin samun lokaci. Kamar ni duk rayuwata ina wani abu na motsa jiki, ko da safe ko da yamma duk tsawon rayuwata. Amma a yanzu sai in je in zauna a ofis in kasa samun lokaci. Kamar kwallon Golf ina bugawa, yanzu yau an yi wajen wata biyar rabona da na buga kwallon Golf.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

Matsala ta hudu: Rashin burge jama'a

Aiki ne wanda duk iyawarka sai wani ya yi korafi, musamman yanzu da aka samu na'ura mai kwakwalwa da kuma yanar gizo wato (internet), dole ne ka je ka samu wani ya kalubalance ka, kuma ba tare da ya san menene ma gaskiyar maganar ba.

Matsala ta biyar: Hulda da 'yan jarida

Ku 'yan jarida abokanan aiki ne, to amma a lokuta da dama za ku zauna da mutum zai fadi magana hanyar da za ku je ku juya maganar nan ku fade ta ta kan kawo matsala.

Mun wallafa wannan labari a shekarar 2018. Mun kara kawo muku shi ne saboda irin kayen da gwamnan Bauchin ya sha a wannan zabe da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel