INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Gwamna Ishaku da zababbun yan majalisan Taraba 24

INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Gwamna Ishaku da zababbun yan majalisan Taraba 24

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta gabatar da takardan shaidan cin zabe ga zababben gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaka

- Ta kuma gabatar da takardar ga zababbun mambobin majalisar dokokin jihar

- Ishaku yayi kira ga al’umman jihar da su bashi kwanciyar hankali don cika alkawarin yakin neman zabe da yayi a lokacin yakin neman zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta gabatar da takardan shaidan cin zabe ga zababben gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaka da mambobin majalisan dokokin jiha 24 a ofishin hukumar zabe da ke babban birnin jihar.

Yayin da yake gabatar da takardun shaidan, Kwamishinan zabe na kasa mai kulawa da jihohin Adamawa, Gombe da Taraba, Ahmed Tijani ya bukaci gwamnan da ya cika alkawarin yakin neman zabe da ya daukarwa al’umman jihar da suka bashi kuri’un su.

Yayi kira ga zababbun mambobin majalisar da su goya wa gwamnatin baya su kuma ba da dokokin da zasu kawo cigaban ga jihar a shekaru hudu masu zuwa.

INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Gwamna Ishaku, da zababbun yan majalisan Taraba 24
INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Gwamna Ishaku, da zababbun yan majalisan Taraba 24
Asali: Twitter

Yayin da yake mayar da martani, Gwamna Darius Ishaku ya yi godiya ga hukumar INEC akan gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da gaskiya da ta yi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Wutar rikicin shugabancin majalisar dattawa a APC na kara ruruwa

Ishaku yayi amfani da bikin wajen kira ga al’umman jihar da su bashi kwanciyar hankali don cika alkawarin yakin neman zabe da yayi a lokacin yakin neman zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel