Shugabancin majalisa: Buhari, gwamnoni da shugabannin APC sun lallashi Goje

Shugabancin majalisa: Buhari, gwamnoni da shugabannin APC sun lallashi Goje

Shugabanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun fara gaggawan dinke duk wata baraka da za ta iya tasowa sakamakon zaben Lawan Ahmad a matsayin shugaban majalisar dattawa.

A jiya Laraba 27 ga watan Maris, Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya gana da daya daga cikin masu neman kujerar majalisa, Sanata Danjuma Goje.

Bayan haka, jiga-jigan jam'iyyar APC da zabubun sanatoci sun gana da Goje domin tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ba ta hure masa kunne ba.

An gano cewa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da magoya bayan Lawan sunyi taro da daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin majalisar, Sanata Ali Ndume domin lallashinsa ya amince da Lawan.

DUBA WANNAN: Takarar kujerar DSP: Sanatoci 56 suna goyon baya na - Kalu

Zaben shugabancin majalisa: Shugabanin APC sun lallashe Goje
Zaben shugabancin majalisa: Shugabanin APC sun lallashe Goje
Asali: Twitter

Shima jagora a majalisa, Sanata Abdullahi Adamu da ke sha'awar takarar shugabancin majalisar ya janye ya goyi bayan Lawan saboda shugaban kasa ya yi na'am da takararsa.

Shugaban kasa da gwamnonin APC da shugabanin jam'iyyar sun kwashe sa'o'i 24 da suka gabata suna kokarin kwantar da duk wata tarzoma da za ta iya tasowa a kan zabin Lawan a matsayin shugaban majalisa.

The Nation ta ruwaito cewa anyi tarukka 11 daga ranar Talata zuwa Laraba domin yin sulhu tsakanin sanatocin APC da ke sha'awar takarar shugabancin majalisar.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta ce, "Muna gab da warware dukkan matsalolin da suka taso sakamakon zaban Lawan. An gudanar da tarurruka a cikin sa'o'i 24 da suka gabata domin ganin an amince da bukatar shugaban kasa da APC.

"A matsayinsa na jagorar jam'iyya shugaban kasa yana kan gaba wurin ganin anyi nasara. Ya tattauna da Goje a kan dalilin da yasa ya zabi Lawan da kuma bukatar kowa ya bashi hadin kai a tsira tare.

"Wasu gwamnonin APC, jiga-jigan jam'iyya da zababun sanatoci suma sun gana da Goje. Muna son kiyaye afkuwar fitina ce domin mun san cewa PDP tana gefe guda tana jira ta ga baraka amma ba zamu bari hakan ya faru ba".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel